Sunday 22 September 2019

Takaitaccen tarihin Janar Mohammadu Buhari

An haifi Janar Muhammadu Buhari a ranar 17 ga watan Disambar shekarar 1942, a garin Daura na jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya. Tauraruwar Janar Buhari ta fara haskawa a lokacin da aka bashi mukamin ministan man fetur da ma'adanai a shekarar 1975, a zamanin mulkin sojin Janar Olusegun Obasanjo. Ko da yake kafin nan shi ne gwamnan sabuwar jahar Arewa maso Gabas da Janar Murtala Ramat Muhammed ya kirkiro. Daga bisani kuma aka nada shi shugaban kamfanin man fetur na kasar watau NNPC wanda aka fara kafawa a shekarar 1977. A zamanin mulkin Janar Sani Abacha an nada shi shugaban hukumar PTF wadda aka kafa da kudaden rarar man da kasar ta samu a wannan lokacin domin gudanar da ayyukan ci gaban al'umma. Kuma ayyukan da Janar Buhari ya yi wa Najeriya kama daga hanyoyi, asibitoci zuwa makarantu ya sa wasu 'yan Najeriya son ganin ya sake zama shugaban kasar. Sau uku Janar Muhammdu Buhari yana tsayawa takarar shugabancin Najeriya amma kuma bai samu nasara ba. A shekarar 2003 da kuma 2007 ya yi takara a karkashin tutar jam'iyyar ANPP sai kuma a shekarar 2011 ya tsaya takarar a inuwar jam'iyyar da ya kafa watau CPC. A shekarar 2015, kuma shi ne dan takarar jam'iyyar APC wacce hadaka ce ta manyan jam'iyyun adawa a kasar.

Takaitaccen tarihin Janar Mohammadu Buhari

An haifi Janar Muhammadu Buhari a ranar 17 ga watan Disambar shekarar 1942, a garin Daura na jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriy...